1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

CAN ta zargi Jonathan da rashin shawo kan rikicin Boko haram

December 29, 2011

Ƙungiyar kiristocin Najeriya ta zargi gwamnatin kasar da gazawa a ƙƙkarin shawo kan matsalar hare-haren boma-bomai da yanzu haka ke barazanar ta da wani yaƙin addini a ƙasar.

epa02994304 A burned out security vehicle on a road following a bomb blast in Damaturu northern Nigeria 06 November 2011. Attacks over night on 04 November have claimed the lives of over 60 people in northern Nigeria according to reports from the Red Cross. Hundreds have been reported to have fled towns as churches and police have been targetted. The Islamist militant group Boko Haram has claimed responsibility for the attacks. EPA/STR
Matsalar hare-haren 'yan Boko HaramHoto: picture-alliance/dpa

An dai kai ga lallashi da ban haƙuri. Sai dai kuma daga dukkan alamu an gaza kaiwa ga burin shawo kan mabiya na addinin kirista a Tarrayar Najeriya, da suka dubi tsabar idon shugaban ƙasar suka ce masa ya kasa a ƙoƙarin shawo kan aiyyukan 'yayan ƙungiyar Boko haramun mai hari da boma bomai. Ita wannan ƙungiyar ta tace ta kai hari na ramuwar gayya kan wata cocin dake garin madalla dake kusa da Abuja a ranar bikin kirisimatin da ta gabata.

Shugabannin ƙungiyar kiristocin ƙasar ta Nijeriya sun zargi yan uwansu musulmin ƙasar da kuma sarakunan arewacin da kau da ido tare da ƙyale cigaba da kisan kiristocin da a cewar ƙungioyar ke zaman mafi rinjaye a ƙasar ta Nigeria baki daya. Pastor ayo oretjeshafor dai na zaman shugaban kungiyar

Mota ta ƙone ƙurmus sakamakon harin bomHoto: picture-alliance/ dpa

Damuwar kiristoci ta ƙaru bayan amincewar ita kanta gwamnatin cewar tana da masaniyar ko su wanene ke da hannu wajen kai hare haren ba tare da iya kaiwa ga ɗaukar wani matakin kamen shugabannin su dake iya kwantar da hankula kan batun ba.Bayan nazarin salo da sigar hare haren sun yi dai dai da jihadi ga mabiya addinin kirista, abun kuma da ke nufin ɗaura yaƙi da al'ummar kirista da kuma Tarayyar Nijeriya baki ɗaya.”

Daga dukkan alamu yaƙin ne ke shirin kankanma duk da ƙoƙarin gwamnatin ƙasar na kwantar da hankula kan rikicin. An dai ruwaito jikata wasu yara 'yan makarantar allo har bakwai a garin Sapele dake jihar Delta a wani harin da ake yiwa kallo ƙoƙari ne na ramuwar gayya kan hare haren na arewa. Sai dai koma wane irin tasiri sabon rikicin ke iya yi ga makomar ƙasar ta Nigeria,i daga dukkan alamu ƙasar na cikin wata tsaka mai wuyar da aka share kusan shekaru 20 bata ga irin ta. Sai dai kuma a cewar shugaba Jonathan ɗin dai a saurari jawabin a cikin rowan sanyi. Sannan kuma ya mayar da martini a cikin rawar jiki dai lokacin bana fito na fito da juna bane.

Bincike akan harin 'yan Boko HaramHoto: AP

Maganar kai harin ta'addanci baƙo ne a wurin mu. A lokacin da wani ɗan Nigeria a cikin watan disamba na shekara 2009 ya nemi fasa jirgin sama mun yi mamaki kuma ya bamu kunya. Amma a yanzu ya zama zahiri muna da 'yan ta'adda a cikin mu har ma da masu ƙuna irin ta baƙin wake. Dole ne mu zaƙulo su. Amma muna neman haɗin kan ɗaukacin 'yan Nigeria. Shi ya sa muke roƙon shugabannin addinai na musulunci da kiristanci da muyi aiki tare."

Abin jira a gani dai na zaman ƙoƙarin gwamnatin Najeriya da a baya ta sha alƙawarin ganin bayan matsalar ta na kasawa, da yanzu haka kuma ke fuskantar barazanar wani sabon yaƙin addini a ƙasar.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Ahmad Tijani Lawal