1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta cimma matsaya da CSU kan 'yan cirani

Gazali Abdou Tasawa
July 3, 2018

A kasar Jamus jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta cimma yarjejeniya da abokiyar kawancenta ta CSU a kan batun 'yan cirani na kafa sansanonin karbar 'yan cirani a kan iyaka da kasar Austriya.

Fraktionssitzung Union Seehofer Merkel
Hoto: picture alliance/dpa/K. Nietfeld

Jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta cimma yarjejeniya da abokiyar kawancenta ta CSU a kan batun 'yan cirani na kafa sansanonin karbar 'yan cirani a kan iyaka da kasar Austriya. Batun da aka kwashe lokaci mai tsawo ana kai ruwa rana tsakanin jam'iyyun siyasar biyu. Sai dai har yanzu da saura rina a kaba a game da martanin da jam'iyyar SPD ta 'yan gurguzu daya abokiyar hadin gwiwar kawancen gwamnatin wacce ta yi watsi da yarjejeniyar wacce a yammacin wannan Talata aka shirya jam'iyyun siyasar guda uku za su sake tattauna sakamakon da aka cimma. 

Angela Merkel ta ceci gwamatin kawance daga rushewa da kyar da zufar goshi bayan makonni da aka kwashe ana samun sabanin ra'ayin a game da batun bakin hauren tsakanin jam'iyyar CDU da kuma CSU. Yarjejeniyar da aka cimma tsakanin jagoran jam'iyyar ta CSU ta masu ra'ayin 'yan mazan jiya Horst Seehofer da CDU, ta tanadi cewar za a kafa sansanonin karbar  masu neman mafaka a kan iyaka tsakanin Austriya da Jamus. Horst Seehofer jagoran na jam'iyyar ta CSU kana ministan cikin gida na Jamus ya ce sun gamsu:


'' Mun amince da juna bayan tattaunawa mai tsauri tsakanin CDU da CSU mun cimma yarjejeniya karara ta yadda za mu taka wa bakin haure birki a nan gaba a kan iyaka tsakanin Jamus da Austriya.''


Har kawo yanzu dai kafin cimma wannan yarjejeniya masu neman mafaka a Jamus 'yan cirani da kasar ke karba ana raraba su ne a cikin sansanonin 'yan gudun hijira na sassan kasar daban-daban kafin a duba takardunsu. Angela Merkel ta ce bayan wannan yarjejeniya kuma za su kakkafa sansanoni na wucin gadi a Jamus na tattara 'yan ciranin wanda daga baya za su tisa keyar bakin hauren zuwa kasahensu tare da hadin gwiwar kasahensu na asili sannan ta kara da cewar:

Hoto: picture alliance/dpa/B. von Jutrczenka


'' Hakika za mu dau matakai a mataki na kasa tare da hadin gwiwar kasashen bakin hauren na asili da kuma wasu kasashen. Ta yadda za mu kafa sansanoni wucin gadi na safara wadanda daga bisanin za mu rika tattaunawa da kasashen asilin 'yan ciranin masu neman mafaka ta yadda za mu sake mayar da su kasahensu hakan ya yi daidai da tsari na Kungiyar Tarrayar Turai.''

Duk da yake nasarar da Angela Merkel ta cimma ta kubutar da gwamnatinta daga kalubalen da ta fuskanta amma dai manazarta na ganin cewar Merkel jikinta ya yi sanyi. Bayan rikici na cikin gida na kyamar da take fuskanta daga 'ya'yan jam'iyyar yanzu kuma za ta tafi da rauni na fuskantar al'amura da dama na siyasa na doka daga bangaran jamiyyar CSU a nan gaba wanda jagoranta ya dage a kan matsayin kafa sansanonin na kan iya saboda barazanar da jam'iyyarsa take fuskanta a zaben Jihohin na lokacin sanhin hunturu daga jam'iyyar AFD ta masu kyamar baki wacce da sannu a hankali hasashen zaben ke cewa za ta iya doke CSU a zaben na tafe a jihar Bavariya saboda siyasar 'yan ciranin.

Hoto: picture alliance/dpa/K. Nietfeld

Sannan bugu da karin har yanzu liki na iya tashi a game da wannan yarjejeniya da aka cimma domin ko da shi ke ma jagorar jam'iyyar SPD Andrea Nahles daya abokiyyar kawancen CDU ta ce sun ji dadi yadda aka kawo karshen ruwa rana tsakanin jam'iyyun siyasar biyu masu ra'ayin rikau, komai na iya faruwa domin kuwa yau da yamma ne jam'iyyar ta SPD da CDU da CSU za su yi taro tare domin tattauna yarjejeniyar da aka cimma.

Idan dai har jamiyyar SPD ta yi watsi da yarjejeniyar abin da ba a tsamani, babu shakka kokarin Angela Merkel na ceton gwamnati ka iya wargajewa ko da shi ke ba tabbas a kan haka. Ya zuwa yanzu dai abin da ke azimin shi ne siyasar Angela Merkel ta karba bakin 'yan cirani wacce ta soma tun a shekara ta 2015 wadda kawo yanzu ta karbi 'yan gudun hijira sama da miliyan daya  a kanta ta zama tarihi domin kuwa yanzu Jamus za ta rufe kofifinta.