1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

CDU na kan gaba a zaben kananan hukumomin NRW

Ahmed Salisu
September 13, 2020

Jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnati Angela Merkel ta samu damar kasancewa a kan gaba a sakamakon farko da aka fidda na zaben kananan hukumomi da aka gudanar a jihar North Rhine Westphalia da ta fi yawan al'umma a Jamus.

CDU Logo Symbolbild Krise
Hoto: AFP/M. Matzen

CDU din ta samu kashi 36 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Ita kuwa jam'iyyar SPD da ke cikin kawancen jam'iyyu masu mulki ta samu kashi 23.5 cikin 100 yayin da jam'iyyyar nan ta masu rajin kare muhalli ta Green ta samu 18.7 cikin.

Duk da cewar CDU wadda Armin Laschet ke jagoranta a jihar ta North Rhine Westphalia (NRW) na kan gaba, sakamakon wannan zaben ya nuna cewar ta samu koma baya idan aka kwatanta da zaben da aka yi a shekarar 2014. Haka ma abin yake ga jam'iyyar SPD da ke biye mata baya sai da jam'iyyar Greens tagomashi ta samu a wannan jikon idan aka kwatanta da wancen zaben da aka yi.

Koma bayan da CDU din ta samu dai wani babban kalubale ne ga Mr. Laschet wanda ake kallo a matsayin guda daga cikin wadanda za su iya maye gurbin Merkel idan wa'adin mulkinta ya kare a shekara mai kamawa.