1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

CDU ta dinke baraka kan raunin shugabanci

Abdul-raheem Hassan
November 23, 2019

Taron jam'iyyar ya amince da jagorancin Annegret Kramp-Karrenbauer a matsayin shugaba tare da yin watsi da bukatar sake zaben magajin Merkel.

Deutschland | CDU-Parteitag in Leipzig
Hoto: Getty Images/S. Gallup

A wani mataki na nuna alamun dinke barakar da ke neman kunno kai a jam'iyyar CDU ta Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel shugabannin jam'iyyar sun cimma kudurin mara baya ga jagorancin shugabar jam'iyyar Annegret Kramp-Karrenbauer

Bisa al'ada jam'iyyar CDU na fidda wanda zai mata takara ba tare da mambobinta sun yi zabe ba, sai dai a wannan karon rukunun matasa a jam'iyyar sun so a jingine tsohuwar al'adar jam'iyyar domin sake zabe don samarwa jam'iyyar sabuwar makoma.

Yayin taron jam'iyyar na shekara-shekara Annegret Kramp-Karrenbauer ta kare dukkannin tsare-tsare da manufofinta da ake suka, daga bisani taron jam'iyyar ya amince da kudurin jagorancinta.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW