1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

CDU za ta yi babban taro a Berlin

February 26, 2018

Jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta shirya don gudanar da babban taronta yau a birnin Berlin, inda wakilan jam'iyyar za su yanke shawarar amincewa da gwamnatin hadaka da ake sa ran zata jagoranci kasar.

Berlin CDU-Zentrale Konrad-Adenauer-Haus
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Gambarini

Jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta shirya don gudanar da babban taronta yau a birnin Berlin, inda wakilan jam'iyyar za su yanke shawarar amincewa da gwamnatin hadaka da ake sa ran zata jagoranci kasar. Wakilai dubu da daya ne za su yanke wannan shawara ta hanyar zabe, bayan kokarin da shugabar gwamnati Merkel ta yi a ranar Lahadi na daukar sabbin fuskoki a sabuwar majalisar ministocin kasar. Ita ma jam'iyyar adawa ta SPD mai mambobi dubu 460 za ta yi nata babban taron ne a ranar 2 ga watan gobe na Maris, inda ake ganin idan baki bai zo daya ba, to fa za a sake zabe ne a Jamus.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana jerin sunayen wadanda za ta nada ministoci cikin gwamnatin hadakar da jam'iyyarta ta CDU da SPD mai adawa za su yi. Merkel ta bayyana sunayen ministocin ne tun ma kafin bangarorin biyu su kaiga tabbatar da kawancen a hukumance a tsakanin nasu.

Jam'iyyar ta CDU dai ta sarayar da manyan mukaman minista da suka hada da na kudi da kuma harkokin cikin gida, yayin kuma da ake sa ran ta za ta rike wasu shida muhimmai. Angela Merkel ta bayyana fatan cewa ta sabuwar gamayyar, sabuwar gwamnatin Jamus za ta kama hanyar kyautata makoma ta ci gaba.