Ce ce ku ce kan zaben kasar Masar
June 23, 2012Shugaban hukumar zaben Masar Farouk Sultan ya karyata rahotannin cewa hukumarsa za ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da ake takaddama a kai idan an jima.Shugaban hukuman ya fada wa gidan talabijin na kasa cewa har yanzu hukumar tana kokarin gudanar da bincike kan kurakuran da abokan hammayar biyu suka yi zargin an tafka.Haka nan kuma hukumar ta ce za'a bayyana wannan sakamakon ranar Lahadi amma kuma za'a ci gaba da wannan bincike har sai an tantance duk wasu bayanai an kuma yanke hukunci.
Daga farko dai hukumar ta yi niyyar bayyana wannan sakamako tun ranar Alhamis da ta gabata, amma ta jinkirta yin hakan bayan da dan takarar jamiyyar 'yan uwa Musulmi Mohammed Mursy da tsohon Frime Minista Ahmed Shafiq, suka gabatar da korafe-korafe akalla 400 a wuraren jefa kuri'u 100 a duk fadin kasar.Wannan jinkiri ne kuma kawo yanzu, ya yi sanadiyyar komawar masu zanga-zanga dandalin Tahrir inda suke bukatar ganin an yi adalci wajen ba da wannan sanarwa a maimakon makarkashiyar ci gaba da rike mulkin da suke zargin majalisar sojin kasar da kullawa.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Halima Balaraba Abbas