Mahawara kan lafiyar Tinubu
March 24, 2023Kasa da tsawon wata guda da kamalla babban zaben Najeriya, muhawara ta barke cikin kasar bisa ziyarar zababben shugaban kasar zuwa Faransa. Tun kafin zaben dama Tinubun ya fara nuna alamun rashi na lafiyar bayan da ya rika fita wajen kasar cikin sunan nema na lafiya. Sai dai kuma sai bayan kammala zaben hankali na 'yan kasar ya fara karkata zuwa ga lafiya ta sabo na shugaban kasar da ke shirin karbar mulki anan gaba.
Wata ziyarar Tinubun zuwa biranen Landan da na Paris kafin kai wa ya zuwa ga Umara a kasar Saudiya dai na neman tayar da hakarkari cikin kasar da ta sha ba dadi ga batu na lafiya ta masu mulki na kasar. A cikin watan Oktoban shekara ta 2021 alal ga misali Tinubun ya share watanni har guda uku cikin birnin Landan a kokari na neman waraka, kuma ko bayan nan dai an rika kallon tangal tangal da ma alamun makyarkyata ta Tinubun a dandali na yakin neman zabe. To sai dai kuma sabuwa ta ziyarar da tun da farkon fari ta kalli sulalewar Tinubun zuwa wajen kasar kafin dagun kara na kafafen labarai na kasar.
Ziyarar Shugaba Muhammadu Buhari na daya daga cikin batutuwan da aka yi ta mahawara a kai a lokacin shugabancinsa kamar yadda batun rashin lafiyan marigayi Umaru Musa 'Yar Adua shi ma ya ja hankali kan yanayin koshin lafiyarsa. Kwanaki dai dai har 172 ne tsohon shugaban kasar Umar Musa Yar Adua ya kai ga sharewa a tsakanin Jamus da kasar Saudiya a cikin batun na lafiya. Ko bayan shi kansa shugaba Muhammadu Buharin da ya share kwanaki 225 a cikin neman na lafiya a farkon wa'adin mulkinsa. Kokarin rabun kafa ta Tinubun a tsakanin batun na lafiya da mulki na kasar na iya kai wa ya zuwa gagarumi na koma baya ga kasar da ke da jan aikin saita tattali na arziki da na batun tsaron al'ummarta.
Ya zuwa yanzu Abujar na fatan rage zurga-zurga ta shugabannin nata zuwa wajen kasar cikin batun na lafiya tare da wani sabon asibiti irin na zamani a Abuja domin daukaci na masu mulki na kasar.