1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cece ku ce kan sake lalacewar dangantar Nijar da Benin

Gazali Abdou Tasawa ZMA
January 5, 2026

Al'umar Nijar sun soma tofa albarkacin bakinsu a game da sake dagulewar huldar diplomasiya tsakanin kasarsu da makwabciyarta Benin.

Patrice Talon da Janar Abdourahamane TianiHoto: Yanick Folly/AFP/Getty Images, ORTN/TÈlÈ Sahel/AFP

A yayin da wasu ke zargin shugabannin kasashen biyu da rura wutar rikicin da kuma ke haddasa al'ummomin kasashen biyu, wasu na ganin akwai bukatar gaggauta hawa teburin tattaunawa domin shawo kan matsalar ta hanyar lumana da fahimtar juna a maimakon ci gaba da zargin juna daga nesa.

Ko da shi ke kasashen biyu makwabtan juna ba su fito a hakumance suka bayyana abin da ya yi zafi a tsakaninsu ba a baya bayan nan, huldar diplomasiyyar ta sake yin tsami ne bayan da mahukuntan kasar Benin suka dauki matakin koro wasu jami'an diplomasiyyar Nijar biyu daga kasarsu tare kuma da sanar da like ofishin jakadancin kasar ta su a birnin Yamai.

Bayan wannan ne Nijar ta mayar da martani ta hanyar umartar mashawarci na farko na ofishin jakadancin Benin a Nijar na fice daga kasar a cikin awoyi 48. Kuma Alhaji Yacouba Dan Maradi shugaban babbar kungiyar ‘yan kasuwan Nijar masu shigo da kaya daga ketare ta SIEN na ganin Benin ce ta sake yin tsokana a daidai loakcin da ake neman gyara huldar diplomasiyyar kasashen biyu da dama ke tangadi.

Yankin kan iyakar Benin da Nijar a MalanvilleHoto: AFP/Getty Images

Sai dai duk da wannan sabon takun saka da aka shiga, mahukuntan Nijar ba su umarci jakadan Nijar a Benin ya baro kasar ba. Kuma Malam Siraji Issa na kungiyar Mojen na ganin akwai bukatar mahukuntan mulkin sojan Nijar su sake tsarin mu'amalarsu da kasashen musamman makwabta.

To amma Kungiyar FCR mai fafutukar kare hakkin dan Adam da demukuradiyya, a ta bakin shugabanta Malam Soule Oumarou ya ce lokaci ya yi da ya kamata kasashen nan biyu su yi sulhu don amfanin al'ummarsu.

Huldar diplomasiyya tsakanin Nijar da Benin ta tabarbare ne bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar a ranar 26 ga watan Yulin 2023. Sai dai sau da dama kasashen biyu sun yi yinkurin sasantawa saboda huldar kasuwanci da ta dangantakar al'ummar kasashen biyu. To amma ga bisa dukkan alamu, har yanzu dai ba su iya sun kai ga warware wannan matsalar ba.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani