1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Abbas ya janye kalamansa da ya yi

Abdul-raheem Hassan
August 18, 2022

Kalaman shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas na kwatanta matakan Isra'ila da kisan kare dangi, na ci gaba da haifar da martani daga kasashe da dama ciki har da Jamus da Isra'ila

Taron manema labarai Olaf Scholz da Mahmoud Abbas
Taron manema labarai Olaf Scholz da Mahmoud AbbasHoto: Wolfgang Kumm/dpa/picture alliance

Duk da janye kalamansa wadanda suka tayar da kura tare da cewa bai yi su da niyya ko danganta su da kisan kare dangi da ya faru a karnin da ya gabata ba, amma har yanzu kalaman na Mahmoud Abbas na ci gaba da shan suka daga sassan duniya da dama. Amirka da Isra'ila sun danganta kalaman da cewa ya wuce kawai abin kunya. Efraim Zuroff shi ne shugaban kungiyar kare hakkin Yahudawa:

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf ScholzHoto: Michael Sohn/AP/picture alliance

"Ina ganin a fili yake cewa mutane sun yi mamaki sosai, amma bai kamata su yi mamaki ko kadan ba saboda shugaban Falasdinawa Mahmoud Abba bayan ya rubuta takardar digirin-digirgir game da kin amincewa da kisan kare dangi da aka yi wa Yahudawa yana musanta kisan kiyashin, kuma ya zo ne domin tabbatar da cewa wani Shugaba na Larabawa na iya fadin abubuwa mafi muni ba tare da hukunci ba."

A nata bangaren gwamnatin Jamus, ba ta tsira ba, Scholz ya sha suka a Jamus da Isra'ila saboda rashin yin tir da kalaman Abbas nan take a taron manema labarai da suka gudanar tare a daren Talata a fadar gwamnatin Jamus. 

A hannun dama Olaf Scholz da Mahmud Abbas a bangaren haguHoto: Wolfgang Kumm/dpa/picture alliance

Sai dai tuni fadar gwamnatin Jamus din ta nuna matsayarta cewa azabtarwa da kisan gillar da aka yi wa Yahudawa miliyan shida a Turai, mummunan laifi ne na cin zarafin dan Adam wanda ba zai misaltu ba. Kakakin shugaban gwamnatin Jamus Steffen Hebestreit ya ce sun fara daukar mataki.

"Ofishin shugaban gwamnatin Jamus ya gayyaci shugaban ofishin jakadancin Falasdinu da ke birnin Berlin, kuma mai bai wa shugaban gwamnati shawara kan harkokin waje da tsaro, shi ma ya isar da wannan sako ba tare da wata shakka ba. Shugaban gwamnatin Jamus na sa ran shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya amince da aukuwar kisan kiyashi kan Yahudawa ba tare da wani sharadi ba. Saboda kalamansa sun haifar da rudani a dangantakar Jamus da hukumar gudanarwar Falasdinawa."

Kalaman na zuwa ne makonni kadan kafin gudanar da bikin cika shekaru 50 da harin Munich, inda wasu Falasdinawa suka kashe 'yan wasan Olympics na Isra'ila 11.