Matsaloli kan kafa majalisa a Jamhuriyar Nijar
April 22, 2025
A Jamhuriyar Nijar yayin da ya kasar a sassa daban-daban suke cece-kuce wajen zaben wadanda za su wakilici al'ummar kasar a majalisar shawara ta rikon kwaryar kasar, shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Janar Abdourahamane Tiani, ya sanya hannu a kan wata doka da ke bayyana manufa, tsari da kuma hanyoyin gudanar da majalisar wanda ya ce mambobinta za su kasance mashawarta ne ba wai za su samu matsayi na ‘yan majalisar dokoki ba.
Karin Bayani: Janar Tiani ya karbi rantsuwar wa'adin jagorantar Nijar
Ganin irin dambarwar da aka sha ko ake sha wajen wakilta wadanda za su halarci wannan majalisa ta shawara ta kasa, kuma ganin kudirin doka da shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar ya dauka da ke kayyade ayyukan majalisar, ya sanya masana da saura masu sharhi yin hannunka mai sanda ga duk masu neman shiga wannan majalisa da su kasance masu kyakkyawar aniya ta aiki domin kasa.
Idan kuwa ya kasance ba yadda su wannan wakillai suke tsamanin kasancewa ba ne a cikin wannan majalisa, ganin cewa babu wata riga. Ta mutunci irin ta yan majalisar dokoki na kasa kuma aikinsu shi ne ba da shawara ga hukumar mulkin soja ta CNSP da gwamnati, ake ganin tun farko da ya kyautu hukumomin su saukaka lamarin.
Sanin kowa ne dai taron kasa da aka yi ya ba da shawarar na a yi shekaru biyar na mulkin rikon kwarya a kasar domin haka ne za a samu damar gyara duk wasu kura-kurai da ke hana ruwa gudu a cikin mulkin siyasa.
Kudirin dokar da Shugaba Abdourahamane Tiani ya saka wa hannu dangane da aikin majalisar, ya tanadi kwamiti-kwamiti da majalisar za ta dukufa aiki a kansu da suka hada da:
Kwamitin da zai kula da Zaman Lafiya, Tsaro, Sasantawa da Hadin Kan Al'umma;
Sai kwamiti da zai kula da sake Kafuwar Siyasa, Al'adu da manyan Cibiyoyi ko ma'aikatu na kasa
Akwai kwamitin kula da harkokin Tattalin Arziki da Ci-gaba mai dorewa;
Gami da kwamitin da zai yi nazari kann siyasar duniya,
Sai kwamitin da zai yi nazari kan harkokin kare hakkin dan Adam da inganta harkokin shari'a, da kuma kwamiti na karshe da zai kula da fannin kiwon lafiya, ilimi da zamantakewar al'umma. Za a wallafa wa al'ummar kasa sakamakon ayyukan majalisar, sannan shawarwarin da majalisar ta bayar a cikin wannan tunani da hangen nesa, za a gabatar da su kai tsaye ga shugaban kasa domin ya yi nazarinsu