1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta fice daga yarjejeniyar Iran

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 10, 2018

A wannan mako, shugaban Amirka ya sanar da ficewar kasarsa daga cikin yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran da aka cimma tsakanin Iran din da kasashe shida masu karfin fada aji a duniya ciki kuwa har da Amirkan.

Bildkombo Donald Trump und Hassan Rohani
Shugaban Amirka Donald Trump da takwaransa na Iran Hassan RohaniHoto: Getty Images/AFP/N. Kamm//A. Kenare

Kasashen Turai sun sha alawashin ci gba da mutunta yarjejeniyar da suka cimma da Iran kan batun makamashin nukiliyarta, duk kuwa da ficewar da shugaban Amirka Donald Trump ya bayyanaa cewa kasarsa ta yi daga wannan yarjejeniya. A shekara ta 2015 ne dai kasashen Amirkan da Rasha da China da Birtaniya da Faransa da kuma Jamus suka cimma yarjejeniya da Iran din kan dakatar da ayyukan da take na bunkasa makamashin nukiliyarta. 

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna