1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Togo: Ko mulkin kasar ya koma na gado?

May 5, 2025

Shugaba Faure Gnassingbé da ya shafe shekaru 20 yana mulki a Togo ya samu damar yin tazarce, bayan da ya aiwatar da tsarin shugabancin kasa da sabon kundin tsarin mulki ya tanada.

Togo | Faure Gnassingbé
Shugaba Faure Gnassingbé na TogoHoto: Filip Singer/EPA POOL/dpa/picture alliance

Duk da cewar an zabi shugaban kasa da ke zama tamkar na jeka na yi ka, amma 'yan adawa na zargin Faure Gnassingbé da samar da tsarin da zai ba shi damar gudanar da salon mulki maras shinge ko iyaka a Togo. Bayan da ya hau kan karagar mulki a watan Fabrairun 2005 sakamakon rasuwar mahaifinsa Etienne Gnassingbe Eyadema da ya shafe sama da shekaru 30 yana mulki a kasar, Shugaba Gnassingbe ya fara kakkange madafun iko ba tare da zabe ba. A cewar masanin kimiyyar siyasa Madi Djabakate kana marubuci dan kasar ta Togo, matakin na kama da tsarin mulkin kama-karya da aka yi daga da zuwa uba da babu alamun kawo  karshensa. Shugaba Faure Gnassingbé ya shafe tsawon shekaru 20 yana mulkin Togo kafin ya kwaskware kundin tsarin mulki, domin ya samu damar yin tazarce. A yanzu haka ma dai, shi ne shugaban gwamnati mai cikakken iko a kasar. David Dossey, mai magana da yawun kungiyar gagwarmaya ta "Togo Debout" ya ce, Shugaba Gnassingbé ya toshe duk hanyoyi da za su iya dakile yunkurinsa na neman ci gaba da kakkange madafun iko.

Shugaban Togo na shekaru 20 Faure Gnassingbé ya sake lashe zaben shugaban kasaHoto: Emile Kouton/AFP

Sai dai tsohon shugaban na Togo kuma sabon shugaban gwamnati Faure Gnassingbé, wanda 'yan adawa ke sukar shi na tasiri a fagen siyasar kasa da kasa. A baya-bayannan ma dai, an nada shi mai shiga tsakani na kungiyar Tarayyar Afirka a rikicin Ruwanda da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Sannan kuma, yana rike irin wannan matsayi a takaddamar da ke tsakanin kasashen AES da kungiyar ECOWAS. Mai magana da yawun kungiyar "Touche pas à ma constitution" ma'ana "Kada ku taba kundin tsarin mulkina" Nathaniel Olympio ya ce, Gnassingbé, mayaudari ne. Mahukuntan Togo na bayyana Faure Gnassingbe a matsayin dan kishin Afirka, wanda nahiyar ta yaba da ayyukansa na mai shiga tsakani. Ministan ma'aikata da kodago da tattaunawa na Togo Gilbert Bawara ya kare shugabansa, tare da cewa akwai abin da ya haifar da sake fasalin kundin tsarin mulki a 2024. 'Yan adawa na Togo da kansu ke rabe dai sun ce, a shirye suke su yaki manufofin mulkin kama karya na Faure Gnassingbé duk da cewa wasu daga cikinsu na gidan kaso a halin yanzu.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani