Cece-kuce kan nada mata mukamun kantoma
July 20, 2017Muhawara na ci gaba da turnukewa a tsakanin malamai da sauran masu fashin baki kan al'amuran da suka shafi al'umma, dangane da batun kin amincewar da majalisar dokokin jihar ta yi na tantance wasu mata da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya nemi a nada su a matsayin shugabannin riko na kananan hukumomin jihar, bisa dalilai na addini da fari dai gwamnan jihar Kano ne ya mika sunayen mutane 36 da yake son nadawa a matsayin kantomomi ciki har da wasu mata guda 2 lamarin da wasu malamai suka yi ta sukar lamirin suna masu cewar hakan ya saba da addini lamarin da ya janyo dole majalisar ta ki amincewa da su, to amma wasu malaman da masu fashin baki na ganin cewar babu wani dalili na addini na hana mata rike mukamai illa dai kawai malaman na kara fito da hanyoyin danne mata.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake samun malamai suna fitar da fatawowin da ke hana mata tsallake wasu iyakoki musamman a tsarin gudanarwar mulki da zamantakewa sai dai kuma a lokuta da dama bakin malaman yakan bambanta da juna dangane da batun bambamcin da ke akwai tsakanin mace da namiji. Yanzu haka dai majalisar dokokin Jihar Kano ta ki tantance sunayen wadannan mata da aka kai domin tantance su a ba su mukamin kantomomi bisa dalilan cewar ya saba da addinin Musulunci. Sai dai kuma masu fashin baki kan lamuran yau da kullum na ganin cewar da fari ma wannan batu tamkar cin fuska ne ga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje wanda ake masa lakabin Khadimul Islama tun da dai suna ganin ya yi nazari kafin tura sunan.
Wani abu da shi ma ke jan hankalin mutane shi ne yadda ake burus da batun wasu matan idan za a nada kan shugabanci, alal misali yanzu haka akanta janar ta kano mace ce, baya ga kwmaishinoni da sauran mata da ke rike da mukamai amma hudubobin malaman ba su shafe su ba.