1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

USA Iran Atomwaffen

Tijani LawalMay 4, 2010

A zauren taron Majalisar Ɗinkin Duniya akan hana yaɗuwar fasahar ƙera makaman ƙare dangi a New York ƙasashen Amirka da Iran sun ƙalubalanci juna da kakkausan harshe

Sakatare-janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki MoonHoto: AP

Tun da farkon fari ne dai aka sa ran fuskantar irin wannan cece-kuce tsakanin ɓangarorin biyu. Duk da cewar akwai tazara ta taswon sa'o'i huɗu a tsakanin jawaban shugaba Ahmadinajad na Iran da sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton sakamakon yawan masu gabatar da jawabai a zauren taron, amma duk da haka sai da suka ƙalubalanci juna da kakkausan harshe tare da barazana. Sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta zargi Iran da laifin keta ƙa'idoji na ƙasa da ƙasa dangane da shirinta na nukiliya kuma a saboda haka tayi kiran ɗaukar tsauraran matakai kan ƙasar. Ta ce duk wanda ke fafutukar ɗaura ɗamarar makaman nukiliya yana mai fatali da yarjejweniyar da ya rattaɓa hannu kanta wajibi ne a ja kunnensa sosai-da-sosai. Ta kuma zargi shi kansa shugaban ƙasar Iran da cewar maƙasudinsa game da halartar zauren taron na New York shi ne ya gurgunta yarjejeniyar dakatar da yaɗuwar fasahar sarrafa makaman ƙare-dangi, amma kamar yadda ta faɗa, haƙonsa ba zai cimma ruwa ba.

A safiyar yau shugaban ƙasar Iran ya sake nanata zarge-zargen da aka gaji ya jinsu akan ƙasar Amurka da sauran ƙasashen dake halartar wannan taro, amma hakan bai zama abin mamaki ba. Iran zata yi iyakacin iyawarta domin karkatar da hankali daga barin gaskiya da kuma musunta duk wani alhakin da ya rataya a wuyanta. Amma fa a ƙarshe za a yanke hukunci ne akan abin da muka aiwatar ba akan abubuwan da muka faɗa ba."

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton a taron manema labaraiHoto: AP

Tun a gabanin haka sai da shugaba Ahmadinajad ya sake nanata musun cewar Iran na ƙoƙarin ɗaura ɗamarar makamai ne na nukiliya a jawabinsa ga wakilan ƙasashe 190 dake da hannu akan yarjejeniyar hana yaɗuwar fasahar sarrafa makaman ƙare-dangi dake halartar taron. Ya ce buƙatar Iran shi ne tayi amfani da fasahar nukiliya don amfanin farar hularta. Amma abin takaici sai ga shi Amurka ta wasu ƙasashe sun kawo batun makaman ƙare-dangi suna yi wa Iran barazana. Bisa ga shugaban na Iran abu mafi a'ala ga ƙasar Amirka shi ne ta mayar da hankali akan matsalolinta na cikin gida.

Shugaba Ahmadinajad na Iran bayan kammala jawabinsa a taron nukiliya a New YorkHoto: AP

Makaman ƙare dangi na farko dai tsofuwar gwamnatin Amirka ce ta kera ta kuma yi amfani da su wajen yaƙar Japan. Kuma duk da cewar wannan matakin ga alamu ya taimaka wa Amirka da ƙawayenta a yaƙin duniya na biyu, amma kuma ya zama ummalaba'isin tserereniyar ƙira makamai tsakanin sauran ƙasashe daga bisani."

Domin adawa da wannan zargin wakilan Amirka da na wasu ƙasashen Turai suka fice daga zauren taron sannan suka sake komawa bayan da shugaba Ahmadinajad ya gama jawabinsa.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Zainab Muhammed Abubakar