Takkadama kan biyan kudin harajin kungiyoyin farar hula
September 20, 2021Hukumar karbar harajin kayayyaki da sauran lamura a Najeriya ce ta bullo da wannan sabon tsari, a ci gaba da fadada hanyar samun kudin shiga da gwamnatin Najeriyar ke yi, inda tace dole ne ga kungiyoyin farar hular su yi rijista da ita domin samun lambar haraji ta TIN da za ta basu ikon biyan haraji ga gwamnati, matakin da ya zo wa kungiyoyin bambarakwai, tare da sanya su maida miurtani cewa bafa zata sabu ba. Alhassan Dantata Mahmood shi ne sakataren kungiyar daya daga cikin kungiyoyin farar hula a Najeriya yana mai cewa. "Wannan matakin cin fuska ne kuma matakin an yi ne da niyar a danne kungiyoyin farar hula, idan ba su da kudade ne a baitul malinsu su san inda za su karbo kudaden ba wai ta 'yan kungiyoyin fararen hula ba."
Karin Bayani: Hanyoyin fita daga matsalar kudi a Najeriya
Daraktan kula da tsare-tsaren haraji na hukumar karbar harajin kayayyaki da sauran al'amura ta Najeriya Mr Temitayo Orebajo da ya bayyana wannan sabon tsari da umurni ya ce nauyi ne na kungiyoyin farar hula su rinka cire haraji daga albashin ma'aikatan da suke dauka, sannan su tattara su mika shi ga gwamnati. Malam Abubakar Ali, masani kan harkar tattalin arziki da ke Abuja, ya ce bai ga aibi ba ga wannan tsarin ba, inda ya ce "Kungiyoyin farar hula wane irin aiki suke yi kuma wadanni kudaden shiga suke samu? Kasuwanci suke ko tallafi suke samu daga waje? Idan har kasuwanci suke kuma yakamata su biya haraji ba su biya to kanan ma ba za su biyan harajin ba."
Karin Bayani: Zakaran gwajin dafi ga tsarin federaliyyar Najeriya
Wannan matakin sabon salo ne ga kungiyoyin farar hulan a Najeriya wai kaza ta ji ana shika da dare, bayan da suka kwashe shekaru ba mai tambayarsu su biya haraji ko da na sisin kwabo. Bisa tsari a najeriya irin wadannan kungiyoyi na samun tallafi ne daga kasashen waje, kuma wannan sabuwar takkadama na nuni da cewa da alamun za a ja daga a tsakanin hukumar da kungiyoyin farar hula a kan wannan batu, domin ko da a baya sabuwar dokar da hukumar ta bullo da ita ta bayyana dole ne wuraren ibada su fara biyan haraji.