Cece-kucen saya wa masarautar Kano motoci
May 6, 2025
Gwamnatin Kano dai ta ce ta dauki wannan mataki ne bisa bin dukkan ka'ídojin kashe kudade da kyautata muradan al'umma don haka 'yan adawa ne kawai ke sukar lamirin matakin
Tun bayan bullar wata takarda mai dauke da tambarin ma' áikatar kananan hukumomi ta jihar Kano wacce ke kunshe da bayanan kashe wadannan kudade don gyara da sayen sabbin motoci ga masarautar Kano, mutane suka ajiye komai suka bude shafin tattaunawa kan wannan batu. Kwamarade Adnan Muktar Tudun wada matashi ne dan gwagwarmaya da ke ganin cewar an saba lamba domin bai kyautu a ware wadannan makudan kudaden don sayen motocin masarauta ba.
Sai dai kuma a ta bakin mashawarcin gwamnan Kano kan harkokin masarauta kuma masanin tarihin masarautar Kano Farfesa Tijjani Muhammad Naniya yana ganin cewar sukar raáyi ne kawai ya sanya yan adawa kuka kan wannan mataki domin tsohuwar magana ce da kowacce gwamnati ke bi, kasancewar tun tale tale an kwace ikon karbar haraji daga hannun sarakuna don haka ne ma ya zama wajibi gwamnati ce za ta ringa kashe musu kudi wajen tafiyar da harkokin su la'akari da cewar dukkan gwamnatocin baya babu wanda bai yi wa masarautar hidima ba.
Malam Ibrahim Ado Kurawa masanin tarihin masarautar Kano ne ya ce wannan mataki ba yau ne farau ba kuma dole ne a yi amfani da kudin gwamnati a biya bukatun masarauta sai dai idan daina sarautar za a yi kacokan
Tuni dai wannan magana ta zama wani babban maudu'í da ke daukar hankali a shafukan sada zumunta musamman a wannan lokaci da ake zaman doya da manja tsakanin magoya bayan sarakuna biyu da ke zuba mulki a Kano.