Ceton masu shaye-shaye a Najeriya
December 28, 2016Talla
Za a iya cewar cewar wannan shi ne karo na farko da aka girka wata cibiyar kyautata halayya ga matasa ‘yan maye a jihar Kanon Najeriyar, wacce ke samar da horon guje- guje da tsalle- tsalle domin dauke hankulan matasan gami da gudanar da bitoci baya ga tallafin shiga makaratu don samun makoma ta gari ga matasan a nan gaba. Dr,Yakubu Maigida Kachako shi ne jagoran wannan cibiya: "To, abin da ya faru ni ina cikin Hukumar Hisba bayan cibiyar da nake yi lokacin da ke cikin hukumar ina ganin yadda ake futa a je a yi kame a kamo yara masu shaye-shaye da sauransu idan ka duba sai ka ga mafiya yawa s marayau ne wasu kuma ya'yan marasa karfi ne. Kuma babban burin da k a gabana shi ne na taimaka wa wadannnan matasa su sami kyakyawar rayuwa.”