1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Chad za ta aike da dakaru 750 zuwa Haiti don taimakawa tsaro

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 24, 2026

MDD ta ce mutane sama da 5,500 suka mutu a Haiti daga watan Maris na 2025 zuwa Janairun 2026 sanadiyyar harin 'yan daba

Yadda masu zanga-zanga a Haiti suka kona tayoyi a kan titi
Yadda masu zanga-zanga a Haiti suka kona tayoyi a kan titiHoto: Arte France

Kasar Chad za ta aike da dakaru 750 na jami'an tsaronta zuwa Haiti, domin tallafawa rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajenta ta sanar yau Talata.

A bara ne Majalisar Dinkin Duniya ta yi wa rundunar kwaskwarima tare da karfafa ta, sakamakon tashin hankalin da kasar ta fuskanta na hare-haren 'yan daba da ke rike da wasu sassan kasar.

Karin bayani: Kara tura 'yan sandan Kenya zuwa Haiti

Alkaluman da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar yau Talata, sun nuna cewa rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 5,500, daga watan Maris na bara zuwa Janairun bana.