1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Chad:Barazanar ambaliya saboda cikar kogunan Logone da Chari

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
October 7, 2024

Firaministan Chadi Allamaye Halina, ya ce babban birnin kasar wato N'Djamena na daga cikin sassan kasar da ke fuskantar wannan barazana ta ballewar kogunan Logone da Chari.

Hoto: Abdullaue Adem/AA/picture alliance

Mahukuntan kasar Chadi sun yi gargadin cewa manyan kogunan kasar guda biyu sun cika sun sun batse, kuma suna barazanar balle wa, sakamakon saukar ruwan saman da aka samu mai yawa a cikin kwanaki goman da suka gabata, wanda ka iya sake haddasa wata mummunar ambaliya.

Firaministan Chadi Allamaye Halina, ya ce babban birnin kasar wato N'Djamena na daga cikin sassan kasar da ke fuskantar wannan barazana ta ballewar kogunan Logone da Chari.

Karin bayani:Ambaliyar ruwa ta hallaka sama da mutum 500 a Chadi

Tun daga watan Yulin da ya gabata ne dai Chadi ke fama da ambaliyar ruwa, da ta daidaita mutane kusan miliyan biyu, bayan rusa gidaje dubu dari da sittin da hudu, da halaka shanu dubu sittin, tare kuma da lalata gonaki masu tarin yawa.

Karin bayani:Ambaliya ta yi barna a Chadi

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ambaliyar ruwa ta halaka mutane sama da dubu daya da dari biyar a kasashen Afirka, da suka hada da Chadi da Nijar da Najeriya, sai Kamaru da Mali da Burkina Faso da kuma Guinea.