1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Chadi: An hana wasu 'yan adawa takarar shugaban kasa

Mouhamadou Awal Balarabe
March 25, 2024

'Yan takarar shugabancin kasa goma ne ke cikin jerin sunayen da kotun kolin ta tantance, yayin da yi watsi da takara wasu goma daga cikin ashirin.

Shugaban mulkin sojin Chadi Mahamat Idriss Deby Itno
Hoto: Denis Sassou Gueipeur/AFP

Daga cikin 'yan takarar da aka amince da su har da shugaban mulkin soja Janar Mahamat Idriss Deby Itno da firaministan yanzu Succes Masra da na tsohon firaminista Pahimi Padacké Albert. Sai dai 'yan kasar Chadi da dama sun yi tir da tsarin da aka bi wajen watsi da wasu manyan 'yan takara.

Kusan dalilai iri daya ne alkalai tara na kotun kare kundin tsarin mulkin kasar Chadi suka bayar, wajen yin watsi da 'yan takara goma a zaben shugaban kasa da zai gudana a ranar 6 ga watan Mayun 2024. Dukkaninsu na da alaka da takardun haihuwa na 'yan takara wadanda ba su dace da tanadin doka ba, kamar rashin daidaito game da wurin da aka haifi dan takara da kuma asalin kasar dan takara. Amma dai  lauya kuma dan rajin kare hakkin dan Adam Jean-Bosco Manga ya ce wadannan hujjoji ba su da tushe da makama.

Karin Bayani: Chadi: An haramtawa 'yan adawa tsayawa takara

Hoto: ISSOUF SANOGO/DENIS SASSOU GUEIPEUR/AFP/Getty Images

"Dalilan suna da ban dariya idan aka yi la'akari da wuraren haihuwar wadannan 'yan takara. 'Yan kasar Chadi ne da ba a haife su a dakin haihuwa na asibiti ba, ko kuma ba a haife su a cibiyoyin da ke da wata karamar hukuma ko ofishin magajin gari da za ta iya yi musu takardar haihuwa da dai sauransu ba. Don haka, ya kamata a yi la'akari da wadannan al'amura wajen yanke hukunci kan takardun haihuwar ‘yan kasar Chadi, don idan haka ne da yawa za su kasance ba 'yan kasar Chadi ba ne."

Mafi akasarin 'yan takarar da aka katse musu hanzari, shugabannin siyasa ne da suka fito daga arewacin Chadi. Wasu sun fito ne daga lardi daya da shugaban gwamnatin mulkin soja Janar Mahamat Idriss Deby kamar Dokta Nassour Koursami. Wannan ne ya sa wasu masu lura da al'amuran siyasa ciki har da Nara Hantoloum, dan jarida na gidan rediyon Liberté  ke ganin cewar, wannan wata dabara ce ta jagoran mulkin soja na zama dan takara dala tilo da ya fito daga Arewa a zaben 6 ga watan Mayun 2024

Karin Bayani: Jam'iyyar MPS ta ayyana Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin 'dan takararta na shugaban Chadi

Hoto: Thomas Coex/AFP

"A cikin wadanda aka ki amincewa, da su, takwas sun kasance ‘yan takara mabiya addinin Musulunci. Wannan ya karfafa zargin da ake yi cewar gwamnatin kasar Chadi ba ta son dan takara daga Arewa da zai kalubalanci Mahamat Deby a zabe. Wannan rashin tantance 'yan takara ya karfafa rade-radin da ake yayatawa cewar za a yi watsi da takarar ‘yan Arewa."

Kiki-kakar kin amincewa da takarar shugabancin Chadi na zuwa ne kasa da wata guda bayan mutuwar babban dan hamayya Yaya Dillo Djérou, wanda sojoji suka kashe a ranar 28 ga watan Fabrairu a wani hari da suka kai hedkwatar jam'iyyarsa PSF. Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta yi kira da a kafa kwamitin bincike mai zaman kansa bisa taimakon kasashen waje saboda mutuwar ta ya haifar da ayoyin tambayoyi game da dalilai na siyasa a yayin da zabe ke dada karatowa.

Duk da cewa, an samu 'yan takara da dama a zaben shugaban kasar Chadi da zai gudana na ranar 6 ga Mayu, amma manazarta da dama sun yi imanin cewa  shugaban gwamnatin mulkin soja ne zai iya lashe zaben, saboda samun goyon bayan jam'iyyun siyasa sama da 200, kuma ya kakkange dukkan hukumomin da ke da alhakin shirya zaben kasar Chadi.