1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi: An kira zanga-zanga a ranar Asabar

May 7, 2021

'Yan adawa a Chadi sun bukaci magoya bayansu da su kasance cikin shiri daga nan zuwa gobe Asabar domin gudanar da wata sabuwar zanga-zangar adawa da gwamnatin soji ta rikon kwarya a kasar.

Weltspiegel 28.04.21 | Demonstration im Tschad | Tableau
Hoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Matakin 'yan adawan Chadi na gudanar da sabuwar zanga-zanga na zuwa ne a daidai lokacin da a yazu haka ake tsare da dimbin mambobinsu da aka kame sakamakon boren da suka gudanar a karshen watan da ya gabata.

Sai dai a nata bangaren majalisar sojin ta wuccin gadi a wajen taronta na farko ta ce babu batun sasanci tsakaninsu da duk wani dan ta’ada da ma masu neman maida masu hannun agogo baya. Haka kuma majalisar ta bayar da sanarwar fatattakar 'yan tawaye daga arewacin kasar ta Chadi in ji ministan tsaron kasar Brahim Daoud Yaya.