1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An hana masu zanga-zanga fitowa a Chadi

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
October 2, 2021

Jami'an 'yan sandan kwantar da tarzoma a Chadi sun tarwatsa wani gungun mutane da suka mamaye harabar wata jam'iyyar adawa a kasar, a yayin da suke shirye-shiryen gudanar da zanga-zanga.

Tschad N'Djamena | Demonstration von Anhängern der NGO Wakit-Tama
Hoto: Blaise Daruistone/DW

Hadin gwiwar kungiyoyin fararen hula da na jam'iyyun siyasar kasar Chadi "Wakit Tama" ne dai suka kira taron gangamin a wannan Asabar a ci gaba da nuna adawarsu da karbe mulki da sojioji suka yi a Chadi. Sai bayan da hukumomi suka amince, daga baya sun kuma bukaci da masu zanga-zangar su bayyana masu taswirar inda masu boren za su biya don daukar mataki na tsaro.

Sojin da suka karbe iko tun bayan mutuwar Shugaba Idriss Déby Itno, sun yi alkawarin shirya zabe a cikin tsukin watanni 18: Tuni kuma suka kaddamar da wata majalisar ministoci mai jagorancin farar hula Albert Pahimi Padacké, ko da yake daukacin wuka da nama kan mulkin na karkashin jagorancin dan marigayi Idriss Déby ne wato Janar Mahamat Déby.