1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChadi

Mahamat Deby, ya lashe zaben shugaban kasa na Chadi

Abdourahamane Hassane
May 10, 2024

Hukumar zabe a kasar Chadi ta ayyana janar Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.

Tschad Übergangspräsident Mahamat Idriss Déby Itno
Hoto: Mikhail Metzel/dpa/AP/picture alliance

 ShugabanChadin ya samu nasara ne shekaru uku bayan ya dare kan karagar mulkin bayan mutuwar mahaifinsa a shekara ta 2021. Deby  ya samu kishi 61%, yayin da  Succes Masara ya samu kishi 18% da digo 58 cikin dari na kuri'un  da aka kada. Tun farko  gabannin hukumar zaben ta bayyana sakamakon Succes Masara ya ikirarin cewar, shi ya samu nasara,yanzu haka kuma ya ce bai amince da sakamakon zaben ba. Jim kadan bayan sanarwar, sojoji sun yi harbi sama a birnin N'Djamena a kusa da cibiyar jam'iyyar Masra domin tarwatsa jama'ar da suka taru.