Chadi na kokarin kulla alakar tsaro da Hangari
September 8, 2024Shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby Itno ya isa kasar Hangari da yammacin ranar Asabar inda ya fara wata ziyarar aiki a wani mataki na karfafa huldar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma shirin tura rundunar sojin Hongary zuwa kasashen yankin Sahel.
Karin bayani: Sahel: Juyin mulki da yakar ta'addanci
Ko da yake ba bu wata sanarwa da ta yi karin bayani a game da makasudin ziyara, to amma manema labarai na cikin gida a Chadi sun ruwaito cewa shugaba Deby zai tattauna da Firaminista Viktor Orban kan yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin tsaro Chadi da Hangari.
A shekarar 2023 da ta gabata dai kasar Hangari ta bayyana aniyarta ta tura tawagar sojoji 200 mai zaman kanta zuwa kasar Chadi domin horar da dakarun kasashen yankin Sahel dabarun yaki da ta'addanci, kuma tun daga wannan lokaci ne hukumomin Hangari suka karfafa alaka da N'Djamena.
Karin bayani: Sojojin Chadi za su raka na Faransa
A hali yanzu dai Chadi ta kasance kasa daya tilo da ta rage a yankin Sahel da ke karbar bakuncin sojojin Faransa da yawansu ya kai 1,000, kuma kulla alakar tsaro da Hangari zai zama tamkar yi wa Paris kishiya ne idan aka yi la'akari da kusancin Hangari da Rasha.