1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Chadi da Mauritaniya sun rusa G5 Sahel

Suleiman Babayo USU
December 13, 2023

Kasashen Chadi da Mauritaniya da suka rage a kungiyar G5 Sahel na yaki da ta'addanci sun amince da rusa kungiyar sakamakon yadda kasashe uku suka fara ficewa daga cikin wannan kawance.

Kawancen tsaron G5 Sahel
Kawancen tsaron G5 SahelHoto: Philippe De Poulpiquet/MAXPPP/dpa/picture alliance

Kasashen biyu da suka rage a cikin kawance tsaron kungiyar G5 Sahel,  Mauritaniya da Chad sun amince da rusa kungiyar baki daya, wadda aka kafa da nufin yaki da kungiyoyi masu nasaba da Jihadi, bayan kasashen uku na Burkina Faso da Mali gami da Jamhuriyar Nijar sun fice tun da farko daga cikin kungiyar.

Karin Bayani: Nijar da EU na neman ja wa ta’addanci birki a Sahel

A shekara ta 2014 aka kafa kungiyar mai mambobin kasashe Mauritania, Chad, Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar. Juye-juyen mulkin soja da aka samu a kasashe uku na Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar sun janyo cikas kan tafiyar da aikin kungiyar musamman na samun tallafi daga kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya.