Barazanar ci gaba da mulkin soji a Chadi
July 10, 2023Watanni 14 kacal suka rage a gudanar da zaben game gari da zummar sake mika mulki a hannun wata zababbiyar gwamnati, kamar yadda aka shata a taswirar gwamnatin rikon kwarya ta mulkin soji. A bisa tsarin, zaben raba gardama ne ke kan gaba daga cikin jadawalin zaben, domin ba wa kasar sabon kudin tsarin mulki a cikin watan Nuwanban wannan shekara, kafin zabukan 'yan majalisun dokoki da na shugaban kasa su biyo baya. Sai dai tun ba a je ko'ina ba kamfanin da aka dora wa alhakin nazari da binciken kundin sunayen masu zabe, ya fara gano wasu tarin kura-kurai a cikin kudin rijistar masu zabe na zamani da ma katin zabe na zamani wato cartes d'électeurs biométriques. Hoinathy Remadj guda ne daga cikin masu bincike a kasar cewa ya yi: "Binciken da kamfanin DocTrust ya yi ya bankado tarin matsalolin da ke bukatar magancewa cikin hanzari tun daga tushe, kama daga batun kayan shirya zabe da ma inda hukumar za ta kafa cibiya da sauransu, duk wannan na nuni da cewar akwai bukatar zuba makudan kudade don tafiyar da wannan aiki, idan kuma aka dubi batun ta wani gefe, za a lura da cewar lokacin da ake bukata na zuba makudan kudaden zai shafi wa'adin da aka dibar wa hukumomin kasar na shirya manyan zabukan."
Bayan matsalar rashin kudi wani cikas shi ne gudanar da zaben lokacin damina
Ko baya ga batun wadatattun kudaden tafiyar da aikin sabinta kudin rijistar sunayen masu zaben, akwai kuma wani kalubalen watan da aka zaba na gudanar da zaben na tantance masu zabe da ma gudanar zaben sabon kudin tsarin mulki, domin kuwa za a gudanar da shi ne a lokacin damina, lamarin da ka iya janyo wa shirin gagarumin koma baya ko ma ya kai ga hana aiwatar da shi baki daya, in ji Christian Baidessou, wani kwararre ta fannin zabe a kasar Chadi: " Dole sai an tattara makudan kudade da wadatattun kayan aiki, yana da matukar wuya a tattara makudan kudaden shirya zabukan a yanzu da galibinsu ke fito mana daga waje, sabili da haka ya sa kara a dunga tunanin zaben na raba gardama a badi maimakon wannan shekara, domin ko damina kawai ba za ta bari a tantance daukacin 'yan kasar daga ko'ina ba wadanda suka cancaci kada kuri'a ba. Kar kuma a manta da cewa akwai wuya a ciwo kan masu hannu da shuni game da btun sake kudin rijistar sunayen masu zabe da zaben raba-gardama ko babban zabe." Kungiyar tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya na taka rawa wajen gudanar da manyan zabukan kasar Chadi tun a shekarar 1996, lamarin da manazarta ke ganin na da matukar wuya ko a wannan karon a zaben ba tare da tallafin kudadensu ba, duba da halin rauni a fannin tallatalin arziki da kasar ta Chadi ke fama da shi.