Chadi: Gangamin adawa da gwamnati
April 5, 2016A dai dai lokacin da jama'a ke gudanar da wannan gangami a birnin N'Djamena da ke zama babban birnin kasar, gwamnatin shugaba Idriss Deby ta tura dubban jami'an tsaro inda suka tarwatsa mahalarta zanga-zangar har ma da kutsa kai a cikin cibiyoyin kwadagon kasar.
Takun saka da cece-ku ce da ke tsakanin kungiyoyin farar hula da gwamnatin kasar ta Chadi ya kara lalacewa, domin ana ci gaba da capke shugabannin farar hular. Sai dai kungiyoyin sun ce babu gudu ba ja da baya dangane da fafutukarsu ta neman a sako musu shugabanni da ke tsare.
Kazalika sun nemi shugaba Idriss Deby Itno da ya janye daga takarar neman tazarce da yake neman yi. Akan hakan ne kungiyoyin ma'aikata da na farar hula suka yi wata hadaka ta nuna cewar "ya ishesu". A kan haka ne suka shirya gangamin na yau, wanda jami'an tsaro suka yi diran mikiya akansu tare da harba musu barkokon sa hawaye da nufin tarwatsasu.