1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jana'izar Shugaban kasar Chadi Idriss Deby

Mohammad Nasiru Awal RGB
April 23, 2021

Shugabanin kasashe duniya da dama sun halarci bikin karrama Shugaba Idriss Deby kafin daga bisani a gudanar da jana'izarsa kamar yadda addinin Islama ta tanadar.

Tschad l Beerdigung des tschadischen Präsidenten Idriss Déby Itno
Hoto: Blaise Dariustone/DW

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya kasance a kasar Chadi inda ya halarci jana'izar shugaban kasa Idriss Deby Itno wanda ya rasu sakamakon raunuka da ya samu a fafatawa da 'yan tawaye. Faransa ta sanya fatanta a kan sabon shugaban kasa Mahamat Idriss Deby, sai dai hakan bai yi wa 'yan adawa dadi ba. Shugaban Faransa Emmanuel Macron da sabon shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby sun zauna kusa da juna a lokacin jana'izar shugaban na tsawon lokaci, Idriss Deby Itno. Macron shi ne kadai shugaban wata kasar yamma da ya halarci jana'izar, sai kuma wasu shugabannin kasashen Afirka, inda ma aka jiyo shi yana cewa: ''Har abada Faransa ba za ta taba bari wani ya kalubalanci kwanciyar hankali da hadin kan kasar Chadi ba, ya kira Deby da aboki kuma jarumin shugaba''  Karin Bayani:  Sabanin fahimta kan makomar Chadi

'Yan adawar Chadi ba za su ji dadin kalamansa ba, sai dai Ahmedou Ould Abdallah mai sharhi kuma dan kasar Mauritaniya ya ce ya ji dadi da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya halarci jana'izar Deby.

Shugaba Macron da Mahamat Idriss DebyHoto: Christophe P. Tesson/Epa/AP/picture alliance

Deby wanda ya mulki Chadi na tsawon shekaru 30 ya rasu a sakamakon raunuka da ya samu a yaki da 'yan tawaye, a cewar sanarwar gwamnati. Faransa wadda ta dauke shi a matsayin daya daga cikin aminanta mafi muhimmanci a Afirka da kuma ke zama kashin bayan yaki da ta'addanci a yankin Sahel, sau biyu tana katsalanda a Chadi domin kare shi. Karin Bayani:  Faransa: Mun yi "rashin mai karfin hali" Bayan ya isa birnin N'Djamena, Macron ya gana da dansa, wanda kuma ya gaji tsohon Shugaba Deby wato Mahamat Idriss Deby da manyan hafsoshin sojin kasar da suka karbi ragamar mulki.

Uwargidan marigayin Hinda Deby ItnoHoto: CHRISTOPHE PETIT TESSON/AFP

 Wato bayan rasuwar Deby. Goyon bayan da Faransa ta nuna wa Deby da rashin yin Allah wadai da karbe mulki da jinginar kundin tsarin mulkin kasa da kuma rusa majalisar dokoki ya janyo suka daga 'yan adawa da kungiyoyin farar hula. Rasuwar shugaban Deby ta jefa kasar da ma yankin na Sahel musamman a fanin yaki da'yan ta'adda cikin rudani, lamarin da ya sanya jama'a tserewa zuwa kasashe makwabta domin tsira da rayukansu. Marigayin ya rasu yana da shekaru 68 wanda kuma ya shafe shekaru 30 yana mulki tun bayan jagorantar juyin mulki a shekarar 1990.

Kawo yanzu ba a kai ga fayyace yadda ya rasa ransa a lokacin ziyarar da ya kai wa dakarunsa da ke yakar 'yan tawaye. Lamarin da ya zo kwana guda bayan sake zabensa a wa'adin mulki na shida. Bikin karrama shugaban kasar Chadi Idriss Déby Itno ya gudana a N'Djamena babban birnin kasar, a gaban shugabannin kasashe da dama. Akwatin gawar Idriss Déby, wanda aka dora a kan dandamali ta kasance a lullube da tutar kasar, inda dogaran fadar shugaban kasa suka kewaye ta a dandalin Place de la Nation.