Kungiyoyin gwagwarmaya sun kafa Jam'iyya
March 20, 2023Kungiyoyin tawayen Chadi kusan 40 ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin mulkin soja a watan Agustan shekarar 2022 a birnin Doha na kasar Qatar. Amma uku daga cikin kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makaman ne kawai suka yanke shawarar rikidewa izuwa matakin siyasa, ciki har da FNDJ da Les Patriotes ta wadanda suka sauya sheka daga majalisar mulkin soja don neman dora Chadi kan turbar dimokuradiyya.
Abdallah Chiddi Djorkodei wanda shi ne shugaban jam'iyyar FNDJustice a kasar Chadi kuma shugaban kwamitin koli da ke bin diddigin kungiyoyin siyasa da na 'yan bindiga bayan cimma yarjejeniyar Doha, ya ce .
"Yarjejeniyar ta ba mu damar sauya kungiyoyinmu na soja ko na 'yan bindiga zuwa ga jam'iyyu ko kungiyoyi na siyasa. Don haka, zabi ya rage wa kungiyoyin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar. Kasancewar mun nuna kishin kasa, mun ga cewa yana da muhimmanci mu canza kungiyarmu ta masu dauke da makamai zuwa jam'iyya, kafin a fara aiwatar da shirin kwance damarar yaki. Sannan muna son ba da gudummawa a wannan lokaci na mulkin rikon kwarya''.
Gwamnatin mulkin sojan Chadi ta yaba matakin rikidewa zuwa jam'iyyun siyasa tare da mika goron gayyata ga sauran kungiyoyin da ke dauke da makamai da su amsa kiran da hukumomin rikon kwarya suka yi musu. Azizi Mahamat Saleh shi ne ministan yada labarai na kasar Chadi kuma kakakin gwamnatin kasar ya yi tsaokaci a kan wannan batu.
“Wani nau'i ne na karfafa dimokuradiyya a kasarmu. Sannan yana ba da damar yin muhawara, maimakon amfani da makamai wajen haddasa rikici. Wannan zai magance matsalolin da ke addabar Chadi tare da bada damar sake gina kasarmu."
Sai dai wasu masu ruwa da tsaki na Chadi na ganin cewar rikidewar wadannan kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai zuwa jam’iyyun siyasa, ba tare da kwance damarar yaki da mayar da su cikin rundunar soja kasar ba zai iya barin baya da kura. Wannan shi ne abin da malamin jami'a Evariste Ngarlem Toldé ke tsoro, inda ya ce yana nufin cewa za a iya mantawa da wasu daga cikin 'yan tawayen.
"Matukar ba a biya mayaka diyya ko an tarwatsa su ba, ina tsoron kada a samu baraka tsakanin wadanda za su zabi rikidewa zuwa jam'iyyun siyasa wadanda za su ci gaba da rike makamansu da kuma wadanda ba za su so shiga wadannan jam'iyyun ba."
Amma dai 'yan tsiraru daga cikin 'yan bindigar ne ke da ra'ayin a fasawa kowa ya rasa. A yanzu haka dai, kungiyoyi 18 na kasar Chadi da ba su rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar ta Doha ba, sun nemi Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Afirka da Kungiyar EU ta Turai da su shirya wata tattaunawar zahiri da za ta kawo zaman lafiya mai dorewa a Chadi.