Chadi: Majalisa ta amince da tswaita wa'adin Deby
April 30, 2018Talla
'Yan majalisar dokokin kasar Chadi, sun rattaba hannu kan kudurin dokar da ke neman yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, dokar dai za ta bai wa shugaba Idriss Deby damar tsawaita wa'adin shugabancinsa har zuwa shekara ta 2033.
A yanzu dai tuni majalisar dokoki ta mika dokar ga shugaban kasa saboda ya saka hannu kafin haka ya zama tabbataciyar doka.