1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 60 da samun 'yanci a Chadi

Abdoulrazak Garba Babani LMJ
August 11, 2020

Kasar Chadi ta samun 'yancin cin gashin kanta daga Turawan mulkin mallakar kasar Faransa, a ranar 11 ga watan Agustan 1960.

Tschad Präsident Idriss Deby Itno
Shugaban mutu ka raba na kasar Chadi Idriss Deby ItnoHoto: DW/B. Dariustone

A tsawon shekaru 60 din da Chadin ta yi da samun 'yancinta daga Faransan, kasar ta fuskanci matsaloli da dama da ke da alaka ta kai tsaye da harkokin siyasa, tun lokacin shugaban kasar na farko François Ngarta Tombalbaye. Siyasa ta kasance ummul aba'isin fara haifar da kabilanci da bangaranci da rikicin addini, wanda har tsawon wadannan shekarun yana tasiri cikin al'amuran kasar, kuma shi ne sanadiyyar haifar da yake-yaken basasa a Chadi.

Umar Adamu Waziri tsohon mukaddashin magajin birnin Ndjamena fadar gwamnatin kasar ta Chadi, kuma tsohon dan siyasa: "Tun da Chadi ta samu 'yncin kanta, an yi zaman lafiya bai fi na tsawon shekaru biyar zuwa shida ba a kasar. A baya ma akwai jam'iyyun siyasa dabam-dabam a kasar, kuma aka suma 'yan tawaye, wato dai ba a samu kwanciyar hankali ba."
Ya kara da cewa, a lokacin mulkin Tambalbaye ne sojoji suka yi juyin mulki suka dauki shugabancin kasar, ba a yi shekaru biyar ba sai yakin basasa ya barke tsakanin shugaban wancan lokaci Janar Felixe Malloum da firaministansa Hissain Habre. Daga bisani aka yi sulhu zuwa Kano karo na daya da karo na biyu, sai kuma Goukkoni Waddai ya zama shugaban kasa, ko da yake Umar Adamu Waziri tsohon mukaddashin magajin birnin Ndjamena fadar gwamnatin kasar Chadin , ya nunar da cewa, shi ma dai dan tawaye Hissain Habre ya zo ya karbe mulki daga hannunsa, inda shi ma Habre shekarunsa bakwai a kan karagar mulki shugaba mai ci yanzu wato Idriss Deby Itno ya karbe mulkin daga hannunsa. 

Shugaban kasar Chadi na farko bayan samun 'yancin kai, François Ngarta TombalbayeHoto: Getty Images/AFP

Shi ma Ibrahim Inuwa mazaunin Ndjamena ne kuma ga abin da yake cewa: "A halin yanzu muna da jam'iyyun siyasa sama da 100 a Chadi, amma kowanne shugaban jam'iyya mutanen kabilarsa ne ke goya masa baya. Ba mu da wata hanya da za mu samu ci-gaba har sai mu mutanen Chadi mun hada kanmu mun bar kabilanci da ya yi katutu a harkokin siyasarmu."

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani