Chadi: Sojoji sun halaka madugun adawa Yaya Dillo
February 29, 2024Dama dai ana bayyana Yaya Dillo Djérou a matsayin babban abokin hamayyar shugaban gwamnatin mulkin sojan Chadi Janar Mahamat Idriss Déby Itno wanda ya dare kan karagar mulki bayan mutuwar mahaifinsa.
A lokacin da yabayyana a gidan rediyo don yin cikakken bayani kan yanayin harin, ministan sadarwa Abderaman Koulamallah ya ba da rahoton mutuwar 'yan sanda hudu da mutuwar mutane uku a cikin 'yan jam'iyyar PSF.
Sanarwar mutuwar Mista Dillo ta zo ne kwana daya bayan tashe-tashen hankula a tsakiyar birnin N'Djamena, inda jami'an tsaro suka yi amfani da bindigogi tare da harba barkonon tsohuwa a kusa da hedkwatar jam'iyyar ta PSF, inda ya fake.
Karin bayani: Hari a Chadi ya hallaka mutane da dama
Gwamnati Ndjamena na zargin Yaya Dillo da kai hari a daren Laraba zuwa Alhamis a hedkwatar hukumar leken asiri ta ANSE, a matsayin ramuwar gayya kan kama dan jam'iyyarsa da aka yi. Wannan harin da Mista Dillo ya kai a cewar gwamnati ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.