1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChadi

Chadi: An kashe Yaya Dillo Djérou

Abdourahamane Hassane
March 1, 2024

Jam'iyyar Yaya Dillo Djérou, babban dan adawa na kasar Chadi, ta zargi sojojin da kashe yaya don kawar da shi daga takarar shugabancin kasar nan da watanni bi

Hoto: AFP/Getty Images

 Gwamnatin Chadin ta musunta zargin kisan na Yaya Dillo Djérou amma magoya bayan jam'iyyar ta 'yan gurguzu ta  (PSF), sun ce kisa ne, da aka tsara domin kauda dan takararsu saboda yana zaman barazana ga Mahamat Idris Deby.Sojojin sun kai hari a gidan dan siyasar ne  da nufin kamashi saboda zargin da ake yi masa, na yunkurin kashe shugaban kotun kollin kasar, amma suka ce  ya ki ya mika wuya, kana ya bude músu wuta kafin daga bisani sun   bindigeshi.