1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaministan Chadi zai fafata da Mahamat Deby a zabe

Abdourahamane Hassane
March 10, 2024

Firaministan da gwamnatin mulkin soja ta Chadi ta nada, Succes Masra, ya sanar da takararsa a zaben shugaban kasa na shida ga watan Mayu.

Hoto: ISSOUF SANOGO/DENIS SASSOU GUEIPEUR/AFP/Getty Images

 Hakan na zuwane kwanaki takwas bayan da shugaban rikon kwarya,Janar Mahamat Idriss Deby Into ya bayyana aniyarsa na tsayawa takara a zaben. Masra wanda tsohon dan adawa ya sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu da Mahamat Deby kafin a nada shi firaminista a ranar daya ga watan Janairu. ‘Yan adawa na kasar sun yi Allah wadai da takara firaministan wanda suka ce tsari ne aka yi domin kara kwarjinin nasara da Mahamat Deby zai samu a zaben. Masra ya bar mukaminsa na babban jami'in a bankin raya Afirka (AfDB) inda ya kafa jam'iyyarsa ta Les Transformateurs a shekarar ta 2018.Ya kuma kasance daya daga cikin manyan masu adawa da Marshal Idriss Deby Itno, wanda 'yan tawaye suka kashe a ranar 19 ga Afrilu,  a shekara ta 2021    bayan shekaru 30 yana mulki.