1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChadi

Chadi ta amince da raka sojojin Faransa kan iyaka

Mouhamadou Awal Balarabe
October 13, 2023

Hukumomin Chadi su yi alkawarin raka sojojin Faransa da aka fatattaka daga Nijar har i zuwa filin jirgin saman N'Djamena inda za su tashi, tare da kare kayan aikinsu har i zuwa iyaka da Kamaru domin jigilar su ta Douala.

Sojojin Faransa na shan kora daga wannan kasa zuwa wancan na yankin sahel
Sojojin Faransa na shan kora daga wannan kasa zuwa wancan na yankin sahelHoto: Sebastien Rieussec/Hans Lucas/IMAGO

Wata sanarwar da babban hafsan sojojin Chadi Janar Abakar Abdelkerim Daoud ya fitar ta nunar da cewar, fadar mulki ta Ndjamena ta amince da bayar da kafar shiga kasarta domin mayar da sojojin Faransa zuwa kasarsu. Dakarun na Faransa za su shafe tafiyar fiye da kilomita 3,000 ta kasa daga Nijar, tare da ratsawa yankunan da ake fama da rikici da wurare da kungiyoyin ta'addanci ke fake kafin su yi bankwana da nahiyar Afirka.

Karin bayani: Fara janye dakarun Faransa

A bisa umurnin gwamnatin milkin sojan Nijar ne,  tawagarsojojin Faransa a Nijar na farko da ta samu rakiyar sojojin Nijar ta bar sansanoninsu na birnin Yamai a ranar talata domin ya da zango a birnin N'Djamena. Kazalika wani kaso na sojoji sun yi amfani da jirage na musamman domin barin kasar ta Nijar.