1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An amince da zaman lafiya a Chadi

Abdul-raheem Hassan
August 8, 2022

Gwamnatin rikon kwarya a Chadi, ta cimma yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyoyin 'yan tawayen 40 na kasar a birnin Doha, matakin na zuwa ne gabanin babban taron sulhu na kasa da za a yi a karshen watan Agusta na 2022.

Chad | Mahamat Idriss Déby
Hoto: Brahim Adji/Tchad Presidential Palace/AFP

Sai dai babbar kungiyar 'yan tawayen kasar ta yi watsi da yarjejeniyar, amma Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar Afirka sun bukaci gwamnatin mulkin soji da Y'an tawayen su yi amfamni da wannan dama wajen kawo dai-daito a kasar don cimma burin kasashen duniya don yakar ta'addanci a yankin Sahel.

Kasar Chadi, daya daga cikin kasashen da suka fi talauci a duniya, ta sha fama da tashe-tashen hankula tun bayan samun 'yancin kai a shekara ta 1960. Shugaban kasar na rikon kwarya Mahamat Idriss Deby, ya yi alkawarin gudanar da tattaunawar kasa da zabe cikin watanni 18 bayan ya karbi ragamar mulkin kasar bayan mutuwar mahaifinsa Idris Deby a fagen daga.