Dokar ta baci a Chadi ta fara aiki
June 3, 2022Talla
Shugaban gwamnatin mulkin soji Mahamat Idriss Deby, ya yi gargadin karuwar hatsari ga al'ummar kasar idan ba a kai agajin jin kai ba Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane miliyan biyar da rabi a yankin Sahel za su iya dogaro da tallafin jin kai a bana. Sakamakon harin da Rasha ta kai wa Ukraine farashin gero ya yi tashin gwauron zabi a bisa kasuwanni. Kusan kashi 30 cikin 100 na alkama da ake samarwa a duniya na zuwa ne daga kasashen biyu wato Rasha da Ukraine.