Chadi ta ce Boko Haram ta fi IS hadari
March 25, 2015 Jakadan Chadi a Majalisar Dinkin Duniya Mahamat Cherif ya bayyana bacin ransa dangane da gaza girka wata runduna ta musamman ta Majalisar ta Dinkin Duniya da za ta yaki kungiyar nan ta Boko da ke gwagwarmaya a Najeriya.
Mr. Cherif ya ce abin takaici ne yadda kwamitin sulhu na Majalisar ta Dinkin Duniya bai maida hankali ba wajen samar da wannan runduna ba don a cewarsa hadarin da ke tattare da Boko Haram ya fi gaban na kungiyar IS.
Kasar Chadi dai na daga cikin kasashen da yanzu haka ke dafawa Najeriya a yakin da ta ke da kungiyar Boko Haram wadda rikicin da ta haifar yai sanadin rasuwar dubban mutane da raba wasu da matsugunansu.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce Jamhuriyar Kamaru na bukatar tallafi daga kasashen duniya don agazwa wanda suka tsere zuwa kasar sakamakon rikicin na Boko Haram.