1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Chadi ta zabtare adadin sojojinta da ke G5-Sahel

August 22, 2021

Chadi ta janye rabin adadin sojojinta da ke cikin rundunar tsaro ta G5-Sahel ta kan iyakokin Burkina Faso da Mali da Nijar. Matakin na nufin Chadin ta janye sojoji 600 daga cikin 1200 da ta jibge a cikin rundunar tsaron.

Mauretanien G5 Sahel Taskforce
Hoto: Getty Images/AFP/T. Samson

Tun a shekara ta 2017 kasashen Sahel biyar ciki da har da Mauritaniya suka kafa rundunar mai yaki da ta'adadnci a yankin, inda Chadi ta tura da wadannan dakaru.

Kakakin gwamnatin Chadi Abderaman Koulamallah ya ce matakin na daga cikin wasu sabbin dabarun yaki da kasar, hadin gwiwa da kungiyar G5 Sahel suka bullo da su.


A yanzu dai Chadi ta bi sahun takwararta Faransa, wace ita ma a baya ta ambaci rage dakarunta masu farautar 'yan ta'addan yankin Sahel daga dubu biyar zuwa kasa da dubu uku, a daidai lokacin da ake shaida karuwar harin ta'addanci a yankin Sahel.