SiyasaAfirka
Chadi ta musanta zargin kashe masunta a Tafkin Chadi
May 15, 2026
Talla
Mutane da dama suka mutu sakamakon mabambantan hare-hare da dakarun sojin Najeriya da kuma na Chadi suka kai a makon da ya gabata. Wasu mazauna yankin Tafkin Chadi sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa sojojin Chadi sun halaka masunta sama da 40 a yankin.
Karin bayani:MDD ta ce a bincika kashe-kashen jama'a a Najeriya da Chadi
Ministan sadarwa na kasar Chadi Gassim Cherif Mahamat bayyana cewa an kitsa labarin ne domin a ragewa dakarun kasarsa karsashi, a kokarinsu na murkushe mayakan Boko Haram. Ministan ya kuma kara da cewa za su kafa kwamitin bincike domin gano gaskiyar lamari kan zargin kashe fararen hula a yankin Tafkin Chadi.