SiyasaAfirka
Chadi ta soke yarjejeniyar tsaro da Faransa
November 29, 2024Talla
Ministan harkokin wajen Chadi Abderaman Koulamallah shi ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na AFP, tare kuma da kira ga Faransar wacce ta yi wa kasar mulkin mallaka da ta mutunta soke yarjajaniyar, kuma wannan mataki bai da alaka da yankar kaunar da kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso suka yi wa Faransa. Akalla akwai Sojojin Faransa 1000 a kasar Chadi.
Karin bayani: Kulla alakar tsaro tsakanin Chadi da Nijar
Faransa dai na fuskantar matsin lamba daga kasashen da ta yiwa mulkin mallaka, baya ga tsamin dangantaka da kasashen AES, a baya bayan nan shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ya sanar da cewa baya bukatar ganin dakarun sojin Faransa a kasarsa.