Chadi ta zargi shugaban Faransa da nunawa Afirka kiyayya
January 7, 2025Kasar Chadi ta zargi shugaban Faransa Emmanuel Macron da nunawa Afirka da shugabanninta kiyayya da rashin martaba su, lokacin da ya ke furta kalaman cewa sun manta su gode wa Faransa, bisa kokarinta na tallafa musu wajen yakar ayyukan ta'ddanci.
Ministan harkokin wajen Chadi Abderaman Koulamallah ya bayyana kalaman Macron din a matsayin kokarin kaskantar da Afirka da shugabanninta, yana mai cewar Afirka da kuma Chadi ne suka yi wa Faransa alfarma a yakin duniya na daya da na biyu don samar mata 'yanci, amma kuma har yanzu ba ta nuna godiya a kai ba, sai suki-burutsu, a don haka tilas ne shugabannin Faransa su koyi dabi'ar darajta al'ummar Afirka.
karin bayani:Faransa ta fara kwashe sojinta daga Chadi bayan yanke hulda
A cikin watan Nuwamban shekarar 2024 ne Chadi ta kori sojin Faransa daga kasarta, sauran kasashen da suka raba gari da uwargijiyar ta su sun hada da Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar, wadanda yanzu haka ke hannun sojoji bayan juyin mulki.
Senegal ma ta bi sahun takwarorinta wajen fatattakar sojin Faransa, har ma firaministanta Ousmane Sonko ke ayyana kalaman shugaban Faransa Macron na rashin godiya a matsayin shaci fadi da kuma kage, domin Faransa ba ta da karfin ikon kare Afirka.
Karin bayani:Huldar tsaro kadai Chadi ta yanke da Faransa
Cote d'Ivore ma ta sallami sojojin Faransa, wadda ke zama ta baya bayan nan da ta dauki wannan mataki.