A nahiyar Turai, aikin yi wa mutane allurar riga-kafin corona yana tafiyar hawainiya, yayin da a nahiyar Afirka a wurare da dama ba a ko fara allurar ba.
Talla
Kasar Chaina na son ta yi amfani da wannan dama ba kawai saboda taimakon jin kai ba, watakila saboda kasuwanci da samun karin angizo a Afirka. Yanzu a fadin duniya an fi bukatar alluran riga-kafin cutar corona. Sai dai na kamfanonin Pfizer da Biontech da Moderna da AstraZeneca sun yi karanci, saboda haka sai kasashe masu arziki ne ke iya samunsu. Kungiyar People's Vaccine Alliance ta ruwaito cewa kasashe masu arziki da ke da kaso 14 cikin 100 na yawan al'ummar duniya, sun saye fiye da rabin alluran masu inganci.
Afirka kuwa na sahun karshe, kuma kungiyar Economist Intelligence Unit ta ce da yawa daga cikin kasashen Afirka, ba za su samu alluran ba har sai watan Afrilun shekarar 2022. Kawo yanzu dai Afirka ta yi odar miliyan 900 na allurar.
Basirar 'yan Afirka kan yaki da cutar Corona
Hukumar Lafiya ta Duniya ta yaba wa 'yan Afirka kan kirkiro hanyoyin yaki da cutar corona a nahiyar. Ga misalin irin kirkira na ceton rai.
Hoto: John Muchucha/AP Photo/picture-alliance
Abin shakar numfashi da aka yi a gida
A birnin Nairobi na Kenya, dalibai masu koyon aikin likita a Jami'ar Kenyatta sun kirkiro na'ura mai kwakwalwa da ke dauke abin da ke taimakon maras lafiya numfashi. Masu bincike a kasashen Afirka suna neman hanyar samun abin da ke taimaka wa numfashi da man goge hannu (sanitizer) sakamakon karuwar bukata a duniya daga kasashe kamar Amirka.
Hoto: John Muchucha/AP Photo/picture-alliance
Mafita mai arha
Vincent Ssembatya, Farfesa a Jami'ar Makerere da ke birnin Kampala na kasar Yuganda, ya kirkiro na'urorin taimakon numfashi masu arha domin taimakon tsarin lafiyar kasar da ke da karancin kudi. Ya hada kai da mai kera mototin Kiira. Ya bayyana dalilin "Kowa na bukatar na'urar, haka ya saka damar Afirka na samu kalilan ne."
Hoto: Prof. Vincent Sembetya
Senegal ta zama cibiyar kirkira
Dalibai masu karanta fannin injiniya a Senegal sun hada kai da gwamnati wajen yaki da annobar corona: Gianna Andjembe yana babban digiri kan fannin injiniyan laturoni ya nuna yadda za a samar da na'ura mai sarrafa kanta ta man goge hannu da ya kirkiro. Daliban suna amfani da fasaha wajen rage tumbatsa a asibitoci.
Hoto: Seyllou/AFP
Dr. Car na duba marasa lafiya
Wannan karamar na'ura mai suna Dr Car, daliban Senegal suka kirkiro. Tana gwada jini da zafin jikin marasa lafiya da ke dauke da corona. Likitoci suna amfani da Dr Car wajen duba marasa lafiya ba tare da kasada ba. Hatta mutanen yankunan karkara ana iya kai wa gare su ta wannan hanyar.
Hoto: Seyllou/AFP
Maganin dauke wuta
A kasar Habasha matashi mai kirkira Ezedin ya kirkiro na'urar taimakon numfashi da mashin da ke dauke da man goge hannu ba tare da an taba jiki ba. Tuni aka fara aiki da abubuwa 13 daga cikin 20 da ya kirkiro. Ana saka sabulu a mashin na wannan hannun da ake takawa yake da na'ura mai kwakwalwa da ke aiki ko an dauke wuta.
Hoto: DW/T. Filate
Amfani da launin fasahar zane
Babu iyaka ga kirkire-kirkire a Afirka. Daga birnin Legas zuwa Nairobi, masu zane-zane na yi kan katanga da gidaje da ke tunatar da mutane muhimmancin ba da tazara, wanke hannu da kyallen rufe baki da hanci. Ana samun irin wannan aiki har a unguwar talakawa ta Kibera da ke Nairobi na Kenya.
Hoto: Getty Images/AFP/S. Maina
Salon kitson corona
Mutane suna tuna wa kansu: Ta hanyar yin salon kitson corona da ba da tazara gami da amfani da kyallen rufe baki da hanci. Sannan suna wanke hannu domin kare kansu, a cewar mai kirkira Mable Etambo a unguwar Kibera da ke Nairobi na Kenya. Suna amfani da launika irin na kwayar cutar.
Hoto: Donwolson Odhiambo
Abinci mai gina jiki har gida
Dokokin hana fita da aka kakaba sun tsauwala wa mutane wajen neman abinci. A birnin Harare na kasar Zimbabuwe an kirkiro fasaha ta sayar da abinci daga manoma zuwa gidaje. Kamfani yana amfani da mashin mai taya uku da tabbatar da tazara, kuma za ka iya sayan kyallen rufe baki da hanci.
Hoto: DW/P. Musvanhiri
Musanyen ilimi lokacin zaman gida
Rufe makarantu a daukacin kasashen Afirka ya hana koyarwa. Ana neman mafita: Misali a Tanzaniya an kirkirro wata manhaja da dalibai za su yi aikin da ita. An ci gaba da aikin da wannan fasaha har bayan sake komawa harkokin rayuwa.
Hoto: Yasuyoshi Chiba/AFP/Getty Images
Gano annoba
Ko'ina, kafofin sada zumunta da zamani sun zama hanyar yaki da corona. A Najeriya da Ghana an kirkiro wata manhaja ta COVID-19 da za ta taimaka wajen gano kasadar kamuwa da corona. Yayin da gwamnatin Afirka ta Kudu ke amfani da manhaja ta WhatsApp da ke ba da amba kan COVID-19. Sannan tsaffin dalibai a Cape Town sun kirkiro manhajar gano labaran karya da ake yadawa.
Hoto: Yanick Folly/AFP/Getty Images
Hotuna 101 | 10
Cibiyar binciken cututtuka masu yaduwa a Afirka ta ce, nahiyar za ta bukaci kimanin miliyan daya da dubu 500 na riga-kafin coronan, domin yi wa kaso 60 cikin 100 na al'umarta allurar riga-kafin da kudinsu gaba daya zai kai dalar Amirka miliyan dubu 10. Wannan abin damuwa ne kamar yadda ministan kiwon lafiya na kasar Kenya Mutahi Kagwe ya shaidawa DW.
Tuni dai Afirka ta Kudu ta samu miliyan daya na allurar riga-kafin kamfanin AstraZeneca daga Indiya. Ruwanda ta yi odar miliyan daya daga kamfanin Pfizer da Moderna na alluran na COVID-19 da ake sa rai za a kai mata a cikin watan nan na Fabrairu. Yuganda kuma na sa ran samun nata alluran daga kamfanonin Moderna da Pfizer da AstraZeneca a cikin watan Afrilu. Hukumar Lafiyar ta Duniya wato WHO, da wani kawance da ake kira GAVI sun dukufa wajen ganin an yi adalci a rabon alluran riga-kafin a kasashe matalauta karkashin wani shiri mai suna COVAX da ke fatan kai allurai miliyan dubu daya da dubu 300 zuwa kasashe masu karamin karfi 92 a karshen shekara. Sai dai alluran da Hukumar WHO ta aminta da su ne kadai, wato kamar na kamfanin Pfizer ke cikin wannan shiri.
Wata matsalar kumma ita ce riga-kafin kamfanonin magungunan na kasashen yamma, ba a yi su saboda yankuna masu zafi ba. Saboda haka wasu kasashen Afirka ke neman alluran riga-kafin daga Chaina, kamar na kamfanin Sinopharm, inji Eric Olander na wani shirin aiki tare tsakanin Chaina da Afirka.
A nasu bangaren Chaina da Rasha na jaddada cewa,za a iya adana alluran riga-kafinsu cikin sauki ba dole ne su kasance a daskare ba. Tun a cikin watan Mayun 2020 shugaban Chaina Xi Jinping ya ce, an bayar da muhimmanci ga yanayin kasashen Afirka wajen samar da alluran riga-kafin na kasarsa. Ko da yake kungiyar EU ta ba wa WHO kudi masu yawa domin samar da alluran ga Afirka, amma tuni Chaina ta shirya tsab wajen raba magungunan. Wato kenan Chaina ka iya samun karin angizo a nahiyar ta Afirka.