1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chaina da Zambiya za su yi amfani da kudadensu

September 15, 2023

Duk da dai kasashen ba su fito fili sun ambaci sunan wani kudi na ketare ba a yunkurin nasu, amma masu sharhi na ganin wani salo ne na Chaina na karya darajar Dalar Amirka da galibin kasashe masu tasowa ke amfani da ita.

Hoto: Sergei Bobylev/dpa/picture alliance

Kasashen Chaina da Zambiya sun sanar da aniyarsu ta fara cinikayya a tsakaninsu da kudaden kasashensu a maimakon kudin wata kasa ta ketare. Wannan na daya daga cikin manyan abubuwan da shugabannin kasashen suka cimma a ganawar da suka yi a Jumma'ar nan.

Hukumomin Beijing da Lusaka sun ce mataki ne da suke sa ran zai rage tsadar kudaden ketaren da 'yan kasuwar kasashen kan saya kafin su kulla wata hada-hadar kasuwanci a tsakaninsu. Chaina da Zambiya sun kuma amince su farfado da cinikayya a bangaren albarkatun kasa da karfafa alaka ta tsaro a tsakaninsu.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani