1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChaina

Tsohon firaministan kasar Chaina Li Keqiang ya mutu

October 27, 2023

Tsohon firaministan kasar Chaina Li Keqiang ya mutu yana mai shekaru 68 da haihuwa sakamakon bugun zuciya kamar yadda kafafan yada labarai na kasar suka ruwaito.

ASEAN Gipfel in Kambodscha | Li Keqiang
Hoto: Mick Tsikas//AAP/IMAGO

Tsohon firaminista kasar Chaina Li Keqiang ya mutu yana mai shekaru 68 da haihuwa sakamakon bugun zuciya kamar yadda kafafan yada labarai na kasar suka ruwaito a safiyar wannan Jumma'a. Li Keqiang fitaccen dan siyasa kuma masanin tattalin arziki ya kasance mataimakin firaminta na tsawon shekaru biyar kafin daga bisani ya dare kan wannan kujera a shekarar 2013 inda ya share shekaru 10 a kan wannan matsayian kafin daga bisani a maye gurbinsa da   Li Qiang a watan Maris din da ya gabata.  

A lokacin da yake rike da mukamin firamininsta Li Keqiangya assasa sauye-sauye ciki har da fasalin siyar kasar Chaina wanda a baya ya ta'allaka kan yarjejeniya, sannan kuma ya kasance na dan gaban goshin shugaba Xi Jinping.A lokacin da yake raye Li Keqiang ya kasance jigo a jam'iyyar CCP mai mulki bayan taronta na shekarar 2012, sai dai burinsa na samar da sauye-sauye a fannin tattalin arziki ya gamu da cikas daga shugaba Xi Jinping wanda hasali ma ya sallamesa daga mukamin firaminista a farko wannan shekara.