1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Fadada matakan takaita zirga-zirga a Chaina

Gazali Abdou Tasawa LMJ
February 4, 2020

Mahukunta kasar Chaina sun fadada matakin takaita zirga-zirga zuwa kusa da birnin Changhai a wani yinkuri na hana yaduwar cutar Coronavirus.

Füssen Touristen mit Mundschutz
Hoto: picture-alliance/dpa/K.-J. Hildenbrand

Mahukuntan kasar Chaina sun sanar a wannan Talata da fadada matakan takaita zirga-zirgar jama'a a kusa da birnin Changhai cibiyar kasuwancin kasar a wani yinkuri na hana yaduwar cutar bayan da a karon farko ta halaka wani mutun daya a Hong-Kong.

 A watan Janerun da ya gabata ne mutumun dan shekaru 39 wanda dama ke fama da matsalolin lafiya ya kai ziyara a birnin Wuhan na kasar Chaina inda a nan ne cutar ta Coronavirus ta bayyana a watan Disemban da ya gabata.

 Domin hana yaduwar cutar yankin na Hong-Kong ya dauki matakin rufe illahirin bodojin kasa ban da wasu gadoji biyu na iyaka da Chaina inda kawo yanzu cutar ta harbi mutane dubu 20 da 400 ta kuma halaka 425, akasari a biranen Wuhan da Hubei inda mahukuntan aksar suka dauki matakin takaita zirga-zirgar jama'a da nufin hana yaduwar cutar.