1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChaina

Kudirin Chaina na hade tsibirin Taiwan

September 22, 2023

China ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da kada ta yi mata katsalandan kan kudirinta na hade tsibirin Taiwan da kasar, sai dai Beijin na son cika wannan buri cikin ruwan sanhi.

China ta jaddada kudirinta na hade Taiwan a zauren taron MDD.Hoto: Mary Altaffer/AP/picture alliance

Mataimakin shugaba kasar Hang Zheng ne ya sanar da hakan a lokacin da yake jawabi a babban zauren taron Majalisar Dinkin Duniya inda ya ce Taiwan wani bangare ne na kasar China da ba ta lamunta ya subuce mata ba.

Karin bayani: Kai ruwa rana tsakanin Taïwan da China

Hang Zheng ya kuma ce babu wanda ya isa ya kawo wa China turjiya kan wannan buri da ta saka a gaba, sannan kuma babu wanda zai hana wa kasar tabbatar da 'yancin yankinta.  

Karin bayani: China za ta nuna karfi a kwace Taiwan

A game da batun yakin Ukraine da Rasha kuwa mataimakin shugaban kasar ta Chaina ya bukaci da a gaggauta tsagaita wuta domin hawa teburin tattaunawa, inda ya jaddada kokarin da kasarsa ke yi don ganin an kawo karshen wannan yaki da aka fara shekara guda da rabi.

Karin bayani: Xi Jinping: China na iya amfani da karfi kan Taiwan