Chaina ta nemi Isra'ila ta daina kashe fararen hula a Gaza
March 7, 2024A yayin da yake bayani ga manema labarai a birnin Beijing a bayan taron majalisar dokokin kasar, Wang Yi ya ce kamata ya yi kasashen duniya su goyi bayan matakan cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta tare da samar da kasar Falasdinu mai cikakken iko.
Karin bayani: An yi gargadin illar yakin Gaza kan tattalin arzikin duniya
Ya ce: "Abin takaici ne kuma abin kunya ne a ce a wannan karni na 21, ba za a iya dakatar da wadannan kashe-kashen bil'adama ba. Bbabu dalilin da zai sa a ci gaba da wannan rikici, kuma babu hujjar ci gaba da kashe fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba."
Karin bayani: Duniya na muradin kafa kasar Falasdinu
Wannan yaki da ma'aikatar lafiya ta Gaza ta bayyana cewar ya yi sanadin mutuwar mutane dubu 30,800, ya shiga wata na shida duk da kokarin da masu shiga tsakani ke yi don magance matsalar jin kai da ake fama da ita a yankin Falasdinawa. Hare-haren bama-bamai da Isra'ila ke kaiwa ba tare da kama hannun yaro ba ya yi sanadiyar mutuwar mutane 83 cikin sa'o'i 24 na baya-bayannan.