1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaZimbabwe

Chamisa: "Ni na lashe zaben Zimbabuwe"

Mouhamadou Awal Balarabe
August 27, 2023

Madugun ‘yan adawar kasar Zimbabuwe Nelson Chamisa ya kalubalanci sakamakon zabe da ya ayyana shugaba mai barin gado Emmerson Mnangagwa a matsayin wanda ya lashe. Ya fito fili ya yi ikirarin samun nasara a wannan zabe.

Madugun adawa na Zimbabuwe Nelson Chamisa ya ce shi ya lashe zabeHoto: Tsvangirayi Mukwazhi/AP Photo/picture alliance

 A yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a birnin Harare,  Nelson Chamisa,wanda Pasto ne kuma lauya mai shekaru 45 da haihuwa, ya ce ya yi matikar mamaki da aka bayyana Emmerson Mnangagwa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar Zimbabuwe, alhali hakikanin sakamakon na nuna akasin haka.

karin bayani: Kammala babban zabe a Zimbabuwe

Hukumar zaben kasar Zimbabbuwe ta nunar da cewa Mnangagwa ya samu kashi 52.6% na kuri'un da aka kada, lamarin da ke ba shi damar gudanar da wa'adi na biyu na mulki, yayin da babban abokin hamayyarsa Nelson Chamisa ya samu kashi 44%. Sai dai masu sa ido na  Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da na (SADC) da Commonwealth suka ce wasu 'yan Zimbabuwe ba su samu damar kada kuri'a ba sakamakon rashin sunayensu a kundin zabe.

Karin bayani: Jam'iyyar CCC ta sha alwashin kayar da Zanu-PF