Chibok: Shakku kan ikirari wata budurwa
March 29, 2016 Wani jami'i da ya zabi a sakaya sunansa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar bisa ga irin bayanan da ta bada da kuma shekarunta da wuya idan kalaman nata gaskiyya ne.
Masu aiko da rahotanni suka ce shekarun yarinyar bai gaza 12 ba yayin da a hannu guda 'yan fafutukar nan ta Bring Back Our Girls suka ce yarinya mafi kankantar shekaru a lokacin da aka sace 'yan matan na da shekara 16 ne.
Nan gaba kadan ne wata tawaga daga Najeriya da ta hada da wasu iyayen 'yan matan na Chibok za su je inda yarinyar ta ke domin tantance ko ta na daga cikin 'yan matan da Boko Haram suka yi awon gaba da su kusan shekaru 2 biyun da suka gabata.
A ranar Jumma'ar da ta gabata ce aka kama wannan yarinya lokacin da ta ke kokarin kai harin kunar bakin wake. Hukumomi dai sun ce yanzu haka ta na karbar magani sakamakon irin raunukan da ta ke da su a jikinta.